Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci a Najeriya ta ce wasu ‘yan siyasa da take zargi da rashawa na
ƙoƙarin ficewa daga ƙasar kafin su sauka daga mulki ranar 29 ga watan Mayu.
EFCC ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani ga Gwamnan Zamfara Bello Matawalle
game da zargin da ya yi wa shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa cewa ya nemi rashawar dala
miliyan biyu a hannunsa – kwatankwacin naira miliyan 922.
EFCC ta ce Gwamna Matawalle ya fara gabatar da zarge-zargen ne bayan ta ƙaddamar da bincike
kan zargin almundahanar naira biliyan 70 a kansa na wasu ayyukan da ta ce an bayar amma ‘yan kwangilar ba su yi ba.
Bello Matawalle na jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar nan na cikin gwamnonin da za su sauka
daga mulki a ranar 29 ga Mayu bayan ya sha kaye a hannun Dauda Lawal na PDP a zaɓen watan Maris da ya gabata.