Ganduje ya mayar da martani kan sautin hirar su dake yawo A kafofin sada zumunta.

Gwamnatin jihar Kano ta yi gargadi da babbar murya ga jama’ar Kano, game da yaɗa barna, yaudara, wuce gona da iri da suka tsiri yi a kwanan nan.

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana hakan da masu aikata hakan a matsayin masu zagon kasa, kuma hakan tamkar wani yunkuri ne da kafafen sada zumunta suke son koya, ta hanyar yaɗa sautin tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Ibrahim Kabiru Masari wadda ta shafi alakarsa ta siyasa da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kwamishinan Yada Labarai da kula da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Malam Muhammad Garba a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa fitar da sautin na matsayin wani yunkuri na wasu bata gari, wadanda ke da manufar tayar da zaune tsaye.

Ya bayyana cewa daga dukkan alamu wasu mutanen da ba su ji dadin doguwar hirar Tinubu tsakanin Ganduje da Masari ba sun dukufa wajen amfani da lamarin don amfanar da kan su da wata mummunar manufa.

Kwamishinan ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC da sauran jama’a da su yi watsi da irin wannan yunkurin kuma su kwantar da hankalinsu da biyayya ga jam’iyyar domin ganin an yi nasarar rantsar da zababben shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *