Buhari ya bayyana babban abinda zai yi kewa sosai bayan ya miƙa mulki

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana babban abinda zai yi kewa sosai bayan ya miƙa
mulki ga sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Shugaba Buhari ya ce bayan ya bar mulki zai yi kewar mutanen da ya yi aiki tare da su a
gwamnatinsa, waɗanda ya kira da mutanen kirki.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a birnin Landan,a cewar hadiminsa na musamman kan
yada labarai, Femi Adesina.

Da ya ke magana kan aikin da ya yi, Adesina ya ce ya hidimtawa shugaban ƙasar iyakar iyawarsa, sannan zai bar Villa a matsayin wanda ya samu cikakkiyar gamsuwa na sauke nauyin da aka ɗora
masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *