FG: “Duk likitan da ya tafi yajin aiki za,a iya maye gurbinsa da wani”

Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar daukar sabbin ma’aikatan wucin gadi da kuma biyan su albashi mudddin likitocin masu neman kwarewar aiki suka shiga yajin aiki.

Ministan kwadago, Chris Ngige, ya yi barazanar maye gurbin likitocin da suka shiga yajin aiki da ma’aikatan wucin-gadi ne a yayin hirarsa da tashar talabijin ta Channels.

Ngige ya yi wannan barazana ce bayan a ranar Laraba Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa (NARD) ta shiga yajin aikin gargadi na kwana biyar kan wasu bukatunta da gwamnati ba ta ci ba.

Bukatun likitocin sun hada da ninka musu albashi sau biyu da ba su sabbin alawus-alawus da kuma biyan su albashin da suke bin bashi gami da alawus dinsu na samun horo.

Amma a martaninsa, Ngige, ya ce ba hakan ba zai yiwu ba, yana mai zargin kungiyar da tsaurin ido ga Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) wadda ke tattaunawa da Gwamnatin Tarayya a kan bukatun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *