Gwamnatin Najeriya ta amince da ƙirƙirar sabbin jami’o’i masu zaman kansu 37 a faɗin ƙasar.
Ministan ilimi na ƙasar Mallam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ga manema labarai, jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwar ƙasar da mataimakin shugaban ƙasar Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar gwamnatin ƙasar.
Sai dai Adamu Adamu bai bayyana sunayen sabbin jami’o’in da majalisar zartarwar ta amince da su ba, to amma ya ce daya daga cikinsu jami’a ce ta da ake karatu ta intanet wadda wata mace daga Bauchi za ta jagoranta Ministan ya ƙara cewa ƙasar na buƙatar ƙarin jami’o’i domin samar da guraben karatu ga miliyoyin matasan ƙasar.