Gwamnatin Najeriya ta gindaya shaarudɗanda wajibi a cikasu gabanin kwaso ragowar mutanen da suka maƙale a Sudan.

Gwamnatin tarayyan Najeriya, a jiya Litinin , ta gindaya shaarudɗan da wajibi a cikasu gabanin kwaso ragowar mutanen da suka maƙale a Sudan.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa FG ta kafa sharuddan ne kan yan Najeriya da sai yanzu suka kawo kansu suna son dawowa gida domin tserewa yaƙin da ya ɓarke a ƙasar Sudan.

Hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje ce ta sanar da sharuɗɗan bayan adadin mutanen da suka taru sun tashi daga 26 zuwa kusan 200.

A cewar hukumar, gwamnati na dab da karƙare shirin jigiƙar wadanda yaƙi ya rutsa da su a Sudan, sai kuma aka samu karin mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *