Gwamnonin jihohi 18 masu barin gado ne za su yi ritaya zuwarayuwarsu ta jin dadi

A kalla gwamnonin jihohi 18 masu barin gado ne za su yi ritaya zuwa rayuwarsu ta jin dadi tare da makudan kudaden fansho duk da karuwar basussuka da kuma rashin biyan albashin ma’aikata.

Bincike ya nuna cewa gwamnonin, wadanda za su mika mulki ga wadanda za su gaje su a ranar 29 ga Mayu, 2023, za su bar bashin akalla Naira tiriliyan 3 da miliyan dari 6 ga gwamnatoci masu zuwa.

Bayanai daga ofishin kula da basussuka na kasa sun nuna cewa adadin bashin da ake bin wadannan jihohin ya hada da rancen cikin gida na Naira tiriliyan 2 da miliyan dubu dari 2 da miliyan dari 7 da kuma rancen dala miliyan dubu 1 da miliyan dari 7 da sha daya daga kasashen waje.

Bashin kasar waje ya kai kusan Naira miliyan dubu 787 da miliyan dari 511, ta hanyar amfani da farashin canjin dala na babban bankin.

Najeriya, wanda ya kasance Naira 460.53 kan kowacce dala a jiya Lahadi.

Adadin bashin ya kasance ne daga watan Disamba 2022, wanda shine sabon adadi da ofishin kula da basussukan ya fitar.

Jihar Kano bayanan sun nuna cewa tana da bashin Naira miliyan dubu 122 da miliyan dari 360 da kuma dala miliyan 100 da dubu 670 na kasashen waje.

Sai dai Ganduje da mataimakinsa suna da hakkin samun kashi 100 na albashinsu na yau da kullun, da gida mai daki shida da kuma yi wa kansu da iyalansu magani kyauta daga ranar 29 ga Mayu, 2023.
Haka kuma dokar da ke jagorantar ‘yancin fansho na tsofaffin gwamnoni da mataimakan gwamnonin ta bayyana cewa za su samu ingantattun ofisoshi don cigaba da harkokinsu na yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *