Zargin cin zarafi: Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya ya bada umarnin kama Seun Kuti

Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ba kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas umarnin kama mawakin Afrobeat Seun Kuti, kan zargin cin zarafin wani dan sanda.

A wani hoton bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a karshen makon nan, ya nuna Kuti yana wanka wa wani dan sanda mari wanda ke sanye da kayan sarki.

Rahotanni sun yi nuni da cewa lamarin ya faru ne akan katafariyar gadar nan ta Third Mainland Bridge da ke Legas a Kudancin kasar.

Sai dai a martanin da mawakin ya mayar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce dan sandan ya yi niyyar kashe shi ne da iyalinsa, sa’annan kuma ya ce yana da shaida kan hakan.

Mawakin kuma ya ce yana maraba da binciken da za a yi a kansa kuma zai bayar da cikakkiyar gudunmawa.

Seun Kuti shi ne dan autan marigayi Fela Kuti, fitaccen mawakin nan na Najeriya wanda ya yi suna a shekarun 1970 da 1980 kuma ya rasu a
shekarar 1997.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *