NAHCON ta amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujerar aikin hajjn bana

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujerar aikin hajjn bana, kamar yadda kamfanonin jiragen aman da za su yi jigilar alhazan suka nema.

Shugaban hukumar Alhzan ƙasar Zikrullah Hassan ne ya tabbatar da haka a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki na hukumar a Abuja babban birnin ƙasar.

Ya ce ”Bayan tattaunawa mai zurfi tare da kamfanonin da za su yi jigilar maniyyatan mun amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujerar aikin hajji ta wannan shekara”.

Kwamishinan kuɗi da ma’aikata na hukumar Nura Hassan Yakasai, ya shaida wa BBC cewa kamfanonin jigilar alhazan ne suka buƙaci hakan saboda yaƙin da ake a Sudan, ya sanya dole sai sun zagaya, ba za su
bi ta sararin samaniyar Sudan ba.

Ya ce kamfanonin jiragen sun ce sai sun yi zagaye na ƙarin sa’o’i biyu, kuma a kowacce sa’a kamfanonin sun ce jiragen kan sha mai na kusan miliyan takwas.

A don haka ne hukumar da kamfanonin jiragen suka amince da ƙarin dala 250 a kan kowacce kujera.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *