Gwamnan jihar Kano Mai barin Gado Dr Abdullahi Umar Ganduje ya shawarci iyaye da kada Neman duniya yasa su manta sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na nemawa yayansu Ilimin addinin musulunci .
Gwamna Dr Ganduje ya furta Hakan ne a nasarautar Rano a yayin Bude musabukar karatun Alkurani Mai tsarki da Gidauniyarsa ta Ganduje foundation ta dauki nauyin shirya a kananan hukumomin jihar
Kano 44 .
Gwamnan Wanda ya samu wakilcin kwamandan Hisba na jihar Kano Sheik Dr Harun Ibn Sina yace matakin farko na Gina rayuwar kananan yara a mahanga ta Neman ilimi da Bude tunaninsu shine Basu Ilimin
Alqurani da sauran litattafan ilimin Musulunci.
Anasa jawabin , Mai martaba Sarkin Rano , Dr Kabiru Muhammad Inuwa ya nemi Hakimai da Dagatai da masu Unguwnni kan su Rika baiwa makarantun addinai hadin Kai da gudun mowar data dace .
A karshe Daraktan Yada labarai na Gidauniyar Ganduje Foundation, Nuhu Gudaji yace Yau za’a Bude musabukar a masarautar Karaye da keyaye .