FG: “Duk shekara ana kashewa kowanne mazaunin gidan yari naira miliyan 1”

Gwamnatin tarayya tace a duk shekara ana kashewa kowanne mazaunin gidan yari naira miliyan 1 a matsayin kudin abinci.

Minstan ya bayyana hakan ne yayinda yake kaddamar da rabon gadajen kwanciya na tallafin cutar Corona ga gidan yarin birnin Fatakwal na jihar Rivers.

Yace irin dawainiyar da gwamnatin tarayya takeyi da daurarru masu laifi yasa gwamnatin ta yanke shawarar mika ragamar cigaba da ciyar da mazauna gidan yarin a hannun gwmanonin jihohinsu.

Yace kashe naira miliyan 1 ga duk wani mazaunin gidan yari a shekara ba karamnin aiki bane da kuma kaluble ga gwmanatin tarayya.

A kowanne wata ana kashewa kowanne mazaunin gidan yari kudi naira dubu 84 kenan a shekara ya kama miliyan 1.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *