Bankin duniya ya kare bukatar Buhari na ciwo bashin dala miliyan 800

Bankin duniya ya kare bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na ciwo bashin karshe na dala miliyan 800 kafin ya bar mulki.

Bankin duniyar yace kasa kamar Najeriya mai yawan mutane fiye da kowacce kasa a Afrika bata da wani zabi illa ta ciwo bashi idan da bukatar hakan musmaman ma shi shugaba Buhari da yace zai cike
gibin kasafin kudin shekarar 2023 da kuma biyan tallafin man fetur.

Daraktan bankin Duniya a Najeriya Shubham Chaudhuri, shine ya bayyana hakan a wata hira da akayi dashi a talabijin a Abuja.

Yan Najeriya sun ta caccaki shugaban kasa Buhari da mukarrabansa akan aniyarsu ta ciwo bashin na dala miliyan dari 8 inda wasu ke cewa bashi ne kawai na sallamar kai ba bashi na ciyar da yan kasa gaba ba.

Yanzu dai bashin da ake bin Najeriya ya tasamma naira Tiliyan 77 idan har bankin na Duniya ya miko bashin da shugaban na Najeriya ya nema na karshe.

Bankin na Duniya yace ko shugaban kasa Buhari ya cire tallafi ko bai cire ba Dole Najeriya ta rayu akan bashi.

Idan za,a iya tunawa jkaridar Biz Point ta rawaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi majalisar kasa data amince masa ya ciwo wannan bashi ne tun a makon da ya gabata saidai lamarin ya tada kura a kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *