An kammala kwaso daliban Najeriya da suka makale a Sudan — NIDCOM

Hukumar da ke kula da ’yan Najeriya mazauna ketare NIDCOM, ta ce an kammala jigilar kwaso ‘yan kasar da suka makale a Sudan da ke fama da rikici.

Hakan na kunshe ne cikin wani sako da hukumar ta NIDCOM ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Asabar.

“A ranar Asabar 13 ga watan Mayu, jirgin Tarco Air ya sauka a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da misalin karfe 8:30 na dare a Abuja, dauke da mutum 147.”

Sanarwar ta kara da cewa an kwaso fasinjojin karshen ne daga filin tashin jirage na kasa da kasa da ke Port Sudan.

“Wannan zangon fasinjoji na karshe shi ne na 15, wanda hakan ya kai jimullar mutanen da Gwamnatin Tarayya ta kwaso zuwa 2,518” a cewar NIDCOM.

“Babu ran dan Najeriya ko daya da ya salwanta ya zuwa yanzu a Sudan” a cewar NIDCOM.

A ranar 15 ga watan Afrilu fada ya barke tsakanin sojoji da dakaru na musamman (RSF).

Daruruwan mutane sun mutu yayin da dubbai suka jikkata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *