Kashim Shettima : Tinubu ba zai maimaita kurkuren Buhari da Jonathan ba.

Mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, Kashim Shettima, ya ce Tinubu ba zai maimaita kurkuren Buhari da Jonathan ba.

Mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, Ya ce kiri-kiri majalisar wakilan tarayya ta hana Buhari cimma abubuwa da yawa a zangon mulkin farko.

Hakannan ya ce tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Jonathan, kirikiri ya gaza shawo kan gwamnatinsa tun da aka wayi gari Aminu Waziri Tambuwal, ya zama kakakin majalisar wakilai.

Wannan dai na zuwa ne bayan da jam’iyyar APC ta sanar da Abbas da Kalu a matsayin yan takarar da take goyon baya.

Haka zalika ya ce shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, bai taɓuka abun a zo a gani ba a zangon mulkinsa na farko saboda rashin tsoma baki a zaben shugabannin majalisa.

Sanata Shettima ya yi wannan bayani ne a wurin ganawarsa da Tajudeen Abbas, Ben Kalu da wasu mambobin, “Join Task,” gamayyar zababbun yan majalisa da suka yi alƙawarin goyon bayan duk wanda APC ta nuna.

Rahotanni sun ce jam’iyyar APC mai mulki ta ɗauki Abbas da Kalu a matsayin ‘yan takarar da take goyon baya a matsayin kakaki da mataimakin kakakin majalisar wakilai a wannan majalisa ta goma da za kafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *