Gwamnati ta kammala tashar samar da lantarki ta zungeru – Ministan wuta

Ministan makamashin wutar lantarki Engr. Abubakar D. Aliyu, ya ce an kammala aikin samar da tashar wutar lantarki mai karfin megawatts 700 dake Zungeru, kuma kamfanin watsa wutar lantarki na Najeriya (TCN) a shirye yake ya karbi wutar da ake yadawa daga tashar samar da wutar lantarkin.

Hakan kuma, in ji shi, zai cike gibin da ake samu a cikin bukatun wutar lantarkin ga yan kasar nan da saurankamfanoni dake gudanar da ayyukan sarrafa ta hanyar amfani da wutar.

Ministan ya bayyana haka ne a jihar Neja a tashar ta Zungeru, yayin da ya kai ziyarar duba aikin tare da mambobin kwamitin majalisar dattawa akan wutar lantarki karkashin jagorancin Sanata Gabriel Suswam da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello.

Engr. Aliyu ya kuma yi nuni da cewa, an yi gwajin dukkan na’urorin da ake amfani da su na injina, kuma an kammala shirye-shiryen kaddamar da aikin a hukumance.

Ya ce karo na karshe da gwamnatin Najeriya ta aiwatar da wani aiki irin na Zungeru Hydroelectric Power tun a shekarar 1960 ya kara da cewa zuba jarin da aka zuba a tashar samar da wutar lantarki ta Zungeru na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na inganta samar da wutar lantarki a fadin kasar nan.

Aliyu ya kuma ce ginin yana daya daga cikin ayyukan da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sa a gaba.

Baya ga samar da karin wutar lantarki ga ‘yan Najeriya, aikin a halin yanzu yana samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya da dama kuma zai samar da hanyoyin magance ambaliyar ruwa, da kuma samar da ruwa.

Shima da yake nasa jawabin, gwamnan Neja ya yabawa shugaba Buhari bisa kammala aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 700 ta Zungeru a Nijar.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin wutar lantarki ya bayyana gamsuwa da aikin, inda ya ce majalisar ta karkashin kwamitinsa ya duba aikin tare da bayar da rahoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *