FRSC: “Ba mu da shirin fara amfanin da dokokin shari’armusulunci wajen hukunta masu karya dokokin tuƙi”

Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadurra ta Kasa FRSC ta nesanta kanta da wani labari da ke cewa hukumar na shirin fara amfanin da dokokin shari’ar musulunci wajen hukunta masu karya dokokin tuƙi da amfani da hanya.

A cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Bisi Kazeem, aka kuma wallafa a shafin hukumar na Tuwita , ta ce wannan labari ba shi da alaƙa da hukumar.

A cikin makon da ya gabata ne dai wasu jaridun ƙasar suka ruwaito wani kwamandan hukumar reshen wata jiha a ƙasar na kira da fara amfani da dokokin shari’ar musulunci ga masu karya dokokin tuƙi a ƙasar.

Yana mai cewa dokokin hukumar sun gaza ta fuskar hukunta masu laifukan, a don haka ne yake kira da hukumar ta fara amfani da dokokin shari’ar musulunci.

To sai dai a sanarwar hukumar ta fitar, ta ce babban kwamandan hukumar na ƙasa Dauda Ali Biu ya umarci kwamandan da ya yi wannan furuci da ya hallara a shalkwatar hukumar da ke Abuja, domin a cewar sanarwar kalaman
nasa sun saɓa dokokin hukumar.
Sanarwar ta ce dokoki da ƙa’idojin da suka kafa hukumar ba dokoki ba ne na
wani addini ko wani yanki na ƙasar.
A don haka hukumar ke kira ga al’umma da su yi watsi da furucin da jami’in
ya yi , tana mai cewa ya saɓa wa dokoki da ƙa’idojin hukumar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *