Buhari da uwar gidansa sun koma “Glass House” da zama gabanin rantsar da Tinubu

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da uwar gidansa, Hajiya Aisha Buhari, sun fara haramar barin mulki, sun koma “Glass House,” gidan shugaban ƙasa mai barin gado da matarsa a cikin Aso Rock.

Rahotanni sun ce Glass House, nan ne gidan da ake warewa shugaban ƙasa da mai ɗakinsa su zauna har zuwa lokacin da zasu bar fadar shugaban ƙasa.

Ana sa ran Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zababben shugaban ƙasa zai kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, 2023 bayan rantsarwa.

Duk da ya koma gidan zababben shugaban kasa da ke ‘Depence House’ a Maitama da ke Birnin Tarayya Abuja.

A wani bidiyo da ta wallafa a shafin ta na Instagram bayan ta jagoranci uwar gidan shugaban kasa mai jiran gado, Remi Tinubu, sun shiga lungu da saƙo, Aisha Buhari ta ce tana fatan za’a kiyaye al’adar miƙa mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *