Atiku Abubakar ya halarci zaman kotun da za a cigaba a yau kan kalubalantar nasarar Tinubu

Tsohon shugaban kasar Najeriya wanda kuma ya yi takarar shugaban kasa a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya halarci zaman kotun da za a cigaba a yau Alhamis kan kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu na APC.

A ranar Talata kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta ɗage zaman da ta fara don ci gaba da zaman share fage a kan ƙorafe-ƙorafe game da nasarar Bola Ahmed Tinubu.

Alƙalan kotun, sun tsara sauraron ƙorafe-ƙorafe daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP da ɗan takararta Atiku Abubakar a yau Alhamis da kuma korafin jam’iyyar LP.

Kotun ta fara zaman sauraron ƙararraki a kan nasarar Bola Ahmed Tinubu ne mako uku daidai kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

Masu ƙorafi huɗu ciki har da manyan ‘yan adawan ƙasar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour, kowannensu yana iƙirarin shi ne ya kamata INEC ta ayyana a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen 25 ga watan Fabrairun 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *