Tinubu zai kai ziyarar aiki kasashen zuwa turai

Zaɓaɓɓen shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar aiki kasashen zuwa Turai a wannan rana

A Wata sanarwa da ofishin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya fitar, na cewa Tinubu zai yi amfani da ziyarar domin lura da shirye-shiryen miƙa mulki da tsare-tsarensa, ba tare da fuskantar damuwa da yawan ɗauke hankali ba.

A yayin ziyarar, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar zai gana da masu zuba jari da manyan abokan hulɗar kasuwanci domin samar da damar zuba jari a ƙasar ƙarƙashin mulkinsa da aka shirya sabbin tsare-tsaren kasuwanci’, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Gabanin tafiyar tasa, Tinubu ya gana da Hon. Tajudeen Abbas da Hon. Benjamin Kalu waɗanda jam’iyyar APC ke mara wa baya domin zama kakakin majalisar wakilan ƙasar da mataimakinsa.

Ana sa ran Tinubu zai koma ƙasar gabanin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban ƙasar ranar 29 ga watan Mayu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *