Osinbajo ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta tarayya na wannan makon a fadar shugaban kasa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta tarayya na wannan makon a fadar shugaban kasa da ke Abuja

Taron na wannan rana, wanda ya fara da karfe 10:00 na safe, taron majalisar ne na gabanin rantsar da sabon shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Ministocin ayyuka na musamman, George Akume, dana Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani, Isa Pantami, ne suka bude taron addu’o’i.

Wadanda suka halarci taron sun hadarda Babban sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha; da Shugabar ma’aikatan gwamnati, Dr Folashade Yemi-Esan, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran sun hadarda ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; dana Kimiyya da Fasaha, Olorunimbe Mamora; da Ministar Kudi Zainab Ahmed; da ministan shari’a, Abubakar Malami,da ministar Ayyukan Jinkai kula da Bala’oi da Ci gaban Al’umma, Sadiya Farouq; Sufuri, da ministan noma Mu’azu Sambo; da ministan lafiya Dr Osagie Ehanire; dana Harkokin Waje, Geoffrey Onyema; dana Wasanni, Sunday Dare,da ministan Sufurin jiragen sama, Hadi Sirika.

Sauran sun hadarda ministan Muhalli, Mohammed Abdullahi; dana Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; kwadago da samar da ayyukan yi, Dr Chris Ngige dana birnin tarayya abuja , Mohammed Bello.

Da Karamar ministar ma’adanai da karafa, Misis Gbemisola Saraki, ita ma ta halarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *