Buhari ya tsawaita zamansa a Landan zuwa mako guda domin duba lafiyar haƙoransa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsawaita zamansa a Landan zuwa mako guda domin duba lafiyar haƙoransa, kamar yadda mai magana da yawunsa Femi Adesina ya bayyana

Shugaban na Najeriya dai ya je Landan ne domin halartar bikin naɗin sarkin Ingila charles lll.

Tun da farko an tsara zai koma Najeriya a cikin wannan mako, sai dai yanzu zai ƙara mako guda domin ganawa da likitan haƙoransa, wanda tuni ya fara duba shi.

Likitan nasa ya buƙaci ya ƙara ganinsa nan da kwanaki biyar domin ci gaba da lura da yanayin haƙoran nasa”, kamar yadda Femi Adesina ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar.

Tun bayan da ya ɗare kujerar shugabancin Najeriya, shugaba Buhari na yawan zuwa Birtaniya kan dalilai na rashin lafiyar da ba a bayyanawa.

A ranar 29 ga watan Mayu ne zai miƙa mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu, bayan kammala wa’adi biyu na mulkinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *