Gwamnati ta samar da gidaje 8,938 a fadin jihohi 35 da Abuja

Gwamnatin tarayya ta ce ta samar da gidaje 8,938 a fadin jihohi 35 da kuma babban birnin tarayya Abuja tare da gina tituna masu tsawon kilomita 9,290 a fadin kasar nan.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana haka a Abuja yayin da yake gabatar da masarorin da ya samu wajen gudanar da aikin sa a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na tsawon shekaru takwas.

Fashola ya ce a shekaru takwas na gwamnatin Buhari an tsara inganta rayuwar ‘yan Najeriya da kuma rage musu radadin talauci.

Ya ce bayan nadin da aka yi masa a matsayin minista, wani bangare na burinsa shi ne inganta rayuwar al’umma ta hanyar samar da manyan ayyuka da za a dade ba a manta da su ba, tare da kammala ayyukan da aka gada daga gwamnatocin baya.

Fashola ya ce gadar Neja ta biyu da gwamnatocin baya suka shafe kusan shekaru talatin ba tare da sun taba su ba, na daya daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin Buhari ta aiwatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *