Hukumar Kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta amince ta Kara Dala 250 ga Alhazan Najeriya saboda Rikicin Sudan.
Karin na zuwa ne bayan yarjejeniyar da aka cimma da Kamfanonin Jigilar Alhazan na Najeriya saboda abinda Suka Kira dole ne su ratsewa kasar ta Sudan Mai fama da rikici
Kamfanonin sunce maimakon su shafe awanni hudu idan za’aje Saudiyya daga Najeriya, a yanzu saboda kaucewa ratsewa ta Sudan za’a iya shafe awanni 7 zuwa 8.