Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar Osun musamman ‘yan siyasa da su marawa Gwamna Ademola Adeleke baya domin samun damar wadata kowa da kowa.
Buhari ya yi wannan bukatar ne a ranar Talata bayan hukuncin da kotun koli ta yanke, wanda ta tabbatar da nasarar zaben gwamnan jam’iyyar PDP, Adeleke a zaben gwamnan jihar Osun da aka yi a watan Yulin shekarar 2022.
Wata sanarwa bayan hukuncin da kotun koli ta yanke ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ta ce:
“Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a ranar 16 ga watan Yuli, 2022, da kuma muhimmiyar rawar da bangaren shari’a ke takawa a zurfafa bin doka da oda.
“Tare da hukuncin karshe da Kotun ta yanke, Shugaban kasar ya tunatar da ‘yan siyasa da magoya bayansu cewa babban aikin da ke gabansu shi ne ganin jama’a su ji tasirin shugabanci nagari, inda za a tabbatar da samun ci gaba, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Osun.
“Saboda haka, ya bukaci daukacin ‘yan kasa da mazauna jihar, musamman manyan ‘ya’yanta maza da mata, da su baiwa gwamnatin Sanata Ademola Adeleke dukkan goyon bayan da take bukata domin ganin an samar da shirye-shirye, manufofi, tsare-tsare da buri na samar da daidaikun mutane da ‘yan kasuwa da bunƙasa nasara.”