Kotu za ta fara zamansauraron ƙararrakin masu neman a rushe nasarar Tinubu yau

Mako uku daidai kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a kasar nan, kotu ta musamman za ta fara zaman sauraron ƙararrakin masu neman a rushe nasarar Bola Ahmed Tinubu a Litinin ɗin nan.

Zaman zai kasance a gaban alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara, waɗanda su ne suka ƙunshi masu shari’a a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta 2023.

Manyan ‘yan adawan ƙasar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour, kowannensu yana iƙirarin shi ne ya kamata INEC ta ayyana a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen 25 ga watan Fabrairun 2023.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta sanar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyya mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaɓen bisa hujjar cewa jam’iyyarsa ta APC ce ta samu ƙuri’u mafi rinjaye da aka kaɗa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *