Kotu ta bayar da umarnin ƙwace kadarorin kwamandan JTF

Babbar kotun tarayya da ke jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya ta bayar da umarnin ƙwace kadarori bakwai a Abuja da guda daya a Bayelsa tare da hannayen jari 30,000 a kamfanin sadarwa na MTN mallakin tsohon kwamandan rundunar hadin gwiwar dakarun tsaro ta JTF Manjo Janar Emmanuel Atewe mai ritaya.

Yayin da yake yanke hukuncin mai shari’a Chukujekwu Aneke ya ce kotu ta ƙwace kadarorin Manjo Janar Atewe – wanda ya jagoranci rundunar dakarun JTF ɗin a yankin Naija Delta – da suka haɗar da gona mai faɗin hecta 50 da ke yankin Kuje a Abuja, da wasu ƙananan filaye da wuraren shaƙatawa a Abuja da Bayelsa.

Hukumar EFCC da ke yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ce dai ta shigar da Mista Ateww ƙara
tare da tsohon daraktan hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta ƙasar Patrick Akpobolokemi, tare da wani mutum bisa zargin haɗin baki wajen sata da almundahar kuɗi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *