“Da gangan na ki yarda na nuna wanda nakeso a zaben tsaida gwanin shugaban kasa na APC”.  — Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce da gangan ya ki yarda ya nuna wanda ya ke so a zaben tsaida gwanin shugaban kasa na APC.

Buhari ya bayyana cewa babu adalci idan ya ba wani mai neman takara fifiko a tsarin damukaradiyya.

Shugaban kasar ya ce ya nemi shugabancin Najeriya sau uku amma duk ya kare a kotu, don haka ba zai iya daga hannun magajinsa ba.

A zaben fitar da ‘dan takara da jam’iyyar APC ta shirya, shugaban kasar bai yi karfa-karfa ba.

Buhari bai nuna wanda yake sha’awar ya samu takara a APC tsakanin irinsu Bola Tinubu, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi da kuma Ahmad Lawan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *