Yankin Alberta na Canada sun ayyana dokar ta-ɓaci biyobayan gobarar daji

Hukumomi a yankin Alberta na Canada sun ayyana dokar ta-ɓaci biyo bayan gobarar daji da ke ta ƙara ruruwa a yankin.

Tuni gobarar ta tilasta wa mutum 24 barin muhallansu.

Mai garin na Alberta Danielle Smith ta ce yanayin iska da zafi su suka ƙara rura wutar.

A halin yanzu dai, gobarar da ta kasu kashi 30 ta kasance barazana ga yankin kuma ana ta aika masu kashe gobara daga wasu yankunan kasar ta Canada zuwa Alberta.

Ayyana dokar ta-ɓacin dai zai taimaka wa hukumomi tsara ayyukansu tare da samun kuɗaɗe na gudanar da aikin jinƙai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *