Tinubu ya taya sabon sarkin Ingila Charles III murna

Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya sabon sarkin Ingila Charles III murnar bikin naɗinsa da aka yimasa a jiya Asabar.

A cikin wata wasiƙar taya murna da Tinubun ya aike wa Sarki Charles lll ya ce a shirye yake domin yin aiki tare da sabon sarkin.

Tinubu ya ce yana da yaƙinin sarkin zai bi sawun mahaifiyarsa Sarauniyar Elizabeth ll, wajen kawo ci gaba a Birtaniya da ƙasashen ƙungiyar rainon Ingila ta Commonwealth.

Zaɓaɓɓen shugaban wanda ke jiran rantsuwar kama aiki, ya ce yana fatan dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya za ta ci gaba daƙarfafa a tsawon zamanin mulkin Sarki Charles lll.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *