Tinubu ya bai wa ma’aikata tabbacin samun kyakykyawan rayuwa a gwamnatinsa.

Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ma’aikata tabba-cin samun kyakykyawan rayuwa a gwamnatinsa.

Ya ce zai ba su fiye da mafi karancin albashi da za su iya gudanar da rayuwarsu da ta iyalansu.

Ya kuma yi alkawarin zama amintaccen aminin ma’aikatan kasar nan da zaran an rantsar da gwamnatinsa a ranar 29 ga Mayun 2023.

Wadannan alkawuran na kunshe ne a cikin sakon bikin ranar ma’aikata na wan-nan shikerar da ya sanya wa hannu.

Da yake tabbatar wa ma’aikatan kasar nan ta hannun kungiyar kwadago (NLC) da kuma kungiyar ‘yan kasuwa (TUC), Tinubu cewa:


“Da zarar an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu a matsayin shugaban Nijeriya, ma’aikata za su samu fiye da mafi karancin albashi”.

“Za ku sami albashi fiye da mafi karancin albashi da za ku iya gudanar da rayuwarku da ta iyalanku”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *