Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya musanta jita-jitar da wasu ‘yan Najeriya ke yi cewa yana sha’awar kujerar shugaban ma’aikata a sabuwar gwamnatin zababben shugaban Najeriyar Bola
Ahmed Tinubu da za a kafa karshen watan Mayun shekarar na ta 2023.
Gwamna El-Rufai ya musanta rade-raden ne a jihar Gombe yayin tattaunawa da manema labarai.
Gwamnan ya je jihar ta Gombe ne domin kaddamar da aikin gina gidaje 550 da gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya zai yi.
El-Rufai ya ce hasashen da mutane ke yi maganganu ne kawai na kan titi.
An ambato gwamnan na Kaduna na cewa ya fi mayar da hankali ne kan samar wa Najeriya ci-gaba maimakon kwadayin wani mukami.
Ya kara da cewa ba dole ne sai mutum ya kasance cikin gwamnati ba kafin ya taimaka wajen ci gaban Najeriya, don haka ko baya cikin gwamnati zai dukufa wajen ciyar da ita gaba a cewarsa.