Yau Kotu Za Ta Yankewa Ekweremadu Da Matarsa Hukunci

A yau ne kotun hukunta manyan laifuka ta Old Bailey da ke Birtaniya za ta yankewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice Ekweremadu da wani likita hukunci.

Wannan ya biyo bayan samun ɗan majalisar dattijan da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam a watan Maris.

Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da ɗan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda, inda ake saran yanke musu hukunci a karon farko a irin dokokin bauta ta zamani.

Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas.

An kaishi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke birnin London.

Yace anyi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai yace ya gane cewar ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *