Rundur ƴan sanda a jihar Kano ta sanar da kama matashin nan Ibrahim Musa da ake zargi ya kashe mahaifiyarsa a birnin Kano.
A wani sako da kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an kama matashin ne a maɓoyarsa dake karamar hukumar Dawakin Tofa na jihar ta Kano.
Kiyawa ya ce matashin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, inda kuma yace yana tu’ammali da ƙwayoyi masu sa maye.
A yanzu haka dai za’a tura shi zuwa kotu bayan kammala bincike.
A jiya ne dai aka ruwaito cewar matashin ya caccakawa mahaifiyarsa mai shekara 50 wuƙa a kanta da ƙirjinta da kuma sauran sassan jiki, inda ya tsere bayan aikata laifin.