Tinubu ya sha alwashin cika dukkanin alƙawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe

Zaɓaɓɓen shugaban Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin cika dukkanin alƙawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe, idan ya hau kan ragamar mulkin ƙasar nan a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne a birnin fatakwal na jihar Rivers, lokacin da ya ke ƙaddamar da ginin harabar kotun majistare, wacce gwamna Nyesom Wike, ya gina.

Tinubu ya yabawa gwamna Wike kan gina harabar kotun, wanda ya bayyana matsayin mai kyau, inda ya yi nuni da cewa babu wata hanyar da ta fi dacewa a yaƙi cin hanci a ɓangaren shari’a, fiye da kula alƙalai da tabbatar da cewa suna cikin walwala.

Tinubu ya yabawa Wike bisa irin ayyukan raya kasa da yake samarwa jihar sa da al’ummar ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *