Majalisa ta bukaci INEC data goge bayanan masu kada kuri’a da sukayi rijista amma suka kasa fitadomin kada kuri’a a zabukan da suka gabata.

Majalisar wakilai ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) data goge bayanan masu kada kuri’a da sukayi rijista, amma suka kasa fita domin kada kuri’a a zabuka biyun da suka gabata.

Majalisar ta yi wannan kiran ne a ranar Alhamis bayan amincewa da kudirin da Leke Abejide ya gabatar, yana mai cewa hakan ya kamata duba da batu daya shafi alumma kai tsaye.

‘Yan majalisar sun yanke shawarar cewa duk wanda bai kada kuri’a ba’a zabukan biyu da aka gudanar a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 18 ga watan Maris za’a goge shi daga rajistar INEC.

Sun kuma yanke shawarar cewa INEC ta samar da wata hanya ta karbarbayanai musamman daga iyalan wadanda sunyi rijistar a baya, amma yanzu kuma sun rasu, domin goge su daga rumbun adana bayanan hukumar.

To sai dai hakan ya gamu da cikas tun a zauren majalisar, Da yake magana kan batun, Nicholas Ossai, ya ce shawarar ta sabawa ka’idar tsarin mulkin 1999.

Yace ‘yancin kada kuri’a batu ne na daban, haka fita domin kada kuri’ar ma abune daban.

Mista Ossai ya bayyana cewa kudirin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasarnan, inda ya kara da cewar zai tauye hakkin ‘yan Najeriya To sai dai Sada Soli na jamiyyar APC a jihar Katsina ya ce kudirin na neman INEC ne kawai ta tsaftace rajistar ta, gabanin zabukan da za’ayi a jihohin Kogi, da Bayelsa da kuma Imo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *