Yanzu haka dai an yankewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, matar sa Beatrice da kuma Dakota Obinna Obeta hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari, kowannensu.
An dai yanke musu hukuncin zaman gidan yarin ne bisa samunsu da laifin cire sassan jikin Bil’adama.