Jakadan Sudan a Najeriya ya roki ‘yan Najeriya dake dawowa daga Sudan suyi hakuri su koma idan al’amura suka lafa.

Jakadan Sudan a Najeriya, Muhammad Yusuf, ya roki ‘yan Najeriya dake dawowa daga ƙasar da ke fama da rikici da suyi hakuri su koma idan al’amura suka lafa.

Jakadan ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis bayan da daruruwan ‘yan kasar suka sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, dake Abuja.

Ana sa ran kwaso ƙarin ragowar yan Najeriya mazauna can a cikin kwanaki masu zuwa.

A nasa jawabin, Yusuf ya ce sun dauki Sudan a matsayin kasa ta biyu, yana mai tabbatar da cewa al’amura sun lafa a birnin Khartoum.

Jakadan ya kuma bayyana fatansa na cewa nan bada dadewa ba sojojin zasu dawo da iko da yankin baki daya.

Ya kara da cewar duk da cewar gwamnati ta sake bada shawarar sake sasantawa, amma ba za’ayi wata tattaunawa tsakanin sojojin da dakarun RSF ba.

A cewarsa yarda da tsagaita bude wuta, don ayyukan jinkai ne kawai zai baiwa mutane damar samun abinci, matsuguni, ruwa da magunguna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *