Majalisar Dokokin Kano Ta Amincewa Ganduje Ya Karbo Wasu Maƙudan Kudin Haraji

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci majalisar dokokin Kano da ta sahalewa gwamnati Kano karbo kudin haraji na Stamp Duties daga gwamnatin tarayya.

Tun da fari dai kungiyar gwamnonin kasar nan ne suka nemi gwamnatin tarayya da ta basu kudin nasu wanda ta rike tun daga shekarar 2015 zuwa 2022.

Gwamnatin tarayya ta amince zata baiwa gwamnoni kudin amma da sharadin sai sun nemi sahalewa daga majalisun dokokin jihohin su, wanda hakan ya sa gwamna Ganduje ya rubuta takarda yana neman majalisar dokokin Kano da ta amince masa ya karbo wadannan kudi.

Da yake jawabi a zauren majalisar shugaban masu rinjaye Labaran Abdul Madari, ya ce kudin kashi uku ne kuma idan majalisar ta amince za a baiwa gwamnati kaso daya a yanzu yayin da za a bayar da ragowar a watanni masu zuwa.

Ya ce idan an karbo kudin za a yiwa al’ummar jihar Kano da kananan hukumomi ayyuka dasu.

Tuni dai Majalisar karkashin kakakinta Hamisu Ibrahim Chidari, ta amince da bukatar gwamnan na karbo wadannan kudi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *