Kungiyar Dalibai Ta Gudanar Da Zanga-zanga A Kano Sakamakon Matsalar Kwacen Waya

Gamayyar Kungiyar Dalibai ta Kasa Reshen Jihar Kano Karkashin Jagorancin Muhyideen Suleiman (BOKA) sun gudanar da Zanga Zangar Lumana a jihar Kano Kan matsalar kwacen waya.

Daliban sun koka ganin yadda mahukunta sukai watsi da lamarin duk da ana rasa rayuka da sassan Jiki, baya ga asarar muhimman bayani da kuma dukiya.

Zanga zangar na a matsayin Jan kunne da kuma jawo hankalin mahukunta, wadda ta gudana a Kofar Ma’aikatar Ilmi dake Jihar Kano, dake Kofar Nassarawa.

Matsalar kwacen waya dai na ci gaba da ƙamari a jihar Kano, lamarin daya sanya hankalin Kowa yake a tashe.

A bangaren hukumomin tsaro kuwa, sun bayyana cewa suna iya bakin kokarin su wajen yaki da matsalar, amma dole sai jama’a sun taimaka musu, ta hanyar taka tsantsan da dukiyar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *