Gwamnati: Rukunin farko na ‘yanNajeriya da za’a ƙwaso daga Saudiyya sakamakon rikicin Sudan za su isa Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce rukunin farko na ‘yan ƙasarnan da za’a ƙwaso daga Saudiyya sakamakon rikicin Sudan za su isa Najeriya.

Shugabar hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna ƙetare Abike Dabiri -Erewa ce ta bayyana haka a Abuja.

Ta ofishin jakadancin Najeriya a Masar ya kammala tattara ‘yan ƙasar da aka kwaso daga Sudan zuwa wani gari da ake kira Aqeel na kusa da kan iyakan ƙasar domin ɗauko su.

Dabiri Erewa tace an kammala shirye-shiryen kwaso ɗaliban daga filin jirgin saman Aswan zuwa Abuja.

Ta ƙara da cewa tuni jirgin saman Air Peace dana rundunar sojin saman ƙasarnan na cikin shiri domin ƙwasar ɗaliban zuwa Abuja bayan kammala tantacewa.

Rikicin da ya ɓarke tsakanin manyan hafsoshin sojin ƙasar Sudan yayi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan mutane, tare da jikkata mutane da dama a birnin Khartoum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *