Gwamnati na ta kare ‘yancin ‘yan jarida dake gudanar da aikinsu a fadin Najeriya — Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta kare ‘yancin ‘yan jarida dake gudanar da aikinsu a fadin kasarnan cikin shekaru takwas na shugabancinsa.

Buhari ya sanar da hakan ne a jiya Talata a yayinda yake taya ‘yan jarida murnar zagayowar ranar bikin ‘yan jarida ta duniya.

Ana dai gudanar da bikin zagoyowar ranar ne, a duk ranar 3 ga watan Mayun kowace shekara.

Taken taron na bana shi ne, ‘Inganta ‘yanci,Bayar da damar fadin albarkacin baki a matsayin ‘yancin dan Adam.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, bikin na wannan shekarar yau shekaru 30 kenan ana gudanar da bikin, tun bayan babban zaman da majalisar dinkin duniya ya fara gudanar da taron, inda ya bayyana cewar nasarar da aka samu tunawa ce ga kwararun ‘yan jarida, musamman wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen fadarawa da kuma ilimantar da ‘yan Najeriya.

Shugaban ya kuma yi kira ga kwararrun ‘yan jaridar dake kasarnan da cewar karsu gajiya wajen ci gaba da nuna kishin kasa a yayain gudanar da aikinsu, musamman don hada kan kasa, inda kuma ya bukace su dasu dinga wanzar da ‘yancin nasu bisa ka’ida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *