Dubu 942 nake karba duk wata a matsayin albashi na — Ngige

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Dakta Chris Ngige, ya bayyana cewa albashin sa da sauran ministocin na kowane wata naira 942,000 bayan an cire na haraji.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake bukatar karin mafi karancin albashi na N30,000 na kasa da kungiyoyin kwadago ke yi.

Ngige, wanda yayi magana a gidan Talabijin na Channels TV’s Politics a ranar Litinin, ya kuma ce ba su da alawus alawus a matsayinsu na minista sai alawus alawus na aiki idan akwai bukatar yin tafiya.


“Abashina N942,000 ne a wata. Albashina tare da PA dina – bayan an cire na haraji – kudin abinci, kudin tafiye-tafiye, albashin mai kula mun lambu na, wanda yake dafa abinci na, duk an haɗa su. Bayan an cire haraji mai yawa, suna biyana N942,000.

“Duk minista da ka gani, shi ne abin da yake; masu ba da shawara na musamman suna samun kusan haka.

Alawus din ba komai ba ne, ba mu da wani alawus sai dai idan kayi tafiya. Kuna iya samun alawus din tafiyar domin gudanar da aiki kamar kowane jami’in gwamnati,” in ji Ngige.

Ya kara da cewa kudaden alawus din tafiye-tafiyen da ministocin ke karba a baya-bayan nan an duba su tare da na sakatarorin dindindin da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *