Za a fara fitar da sakamakon jarrabawar UTME ta 2023 2 ga watan Mayu a — JAMB

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta ce za ta fara fitar da sakamakon jarrabawar UTME ta 2023 daga ranar Talata 2 ga watan Mayu, 2023.

Hakan na kunshe ne acikin wani taro da aka gudanar na gaggawa a karshen mako a Abuja.

Kakakin hukumar ta JAMB, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana sanarwar ga manema labarai a ranar Litinin.
Hukumar ta JAMB ta ce an samu jinkirin fitar da sakamakon ne don samun damar gudanar da cikakken
bincike kan bin dokokin hukumar a lokacin zana jarrabawar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *