Hukumomin Masar sun ƙi buɗe kan iyakarsu ga ɗaliban Najeriya waɗanda ke guje wa rikicin Sudan – NIDCOM

Hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen ƙetare ta ce hukumomin Masar sun ƙi buɗe kan iyakarsu ga ɗaliban Najeriya waɗanda ke guje wa rikicin da ke faruwa a Sudan.

Sai dai hukumar ta ce yanzu haka akwai jirgin sojin Najeriya da ke girke a birnin Aswan, kuma a cewar ta,
jirgin ba zai baro birnin ba sai ya ɗauki ɗaliban na Najeriya.

Har yanzu dai Najeriya na fafutikar ganin yadda za ta iya kwaso dubban ɗalibai da sauran al’ummarta daga Sudan inda faɗa ya ɓarke a makon jiya.

Bayanai na cewa wasu ɗaliban na kan hanyarsu ta zuwa kan iyakar Sudan da Saudiyya, inda ake sa ran za su tsallaka zuwa cikin ƙasar kafin a kwashe su zuwa gida.

Faɗa ya ɓarke ne tsakanin ɓangarorin dakaru masu biyayya da manyan jami’an sojin Sudan biyu.

Tuni ƙasashe da dama suka kwashe al’ummarsu domin gudun kada yaƙin ya rutsa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *