Gwamnatin Tarayya ta fara shirin cefanar da asibitin fadar shugaban kasa

Gwamnatin Tarayya ta fara shirin cefanar da Asibitin Fadar Shugaban Kasa da wasu sassa da ke karkashin fadar gwamnatin ga ’yan kasuwa.

Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa, Tijjani Umar, ya ce Ma’aikatar Kudi da Kasa tare da Fadar Shugaban Kasar sun ware wasu ayyuka da tsare-tsare uku a Fadar

Shugaban Kasa da gwamnati za ta fara yin hadaka da ’yan kasuwa wajen gudanar da su.

Ya bayyana cewa Asibitin Fadar Shguaban Kasa da ke Abuja da Legas daya ne daga bangarorin da ake shirin shigo da ’yan kasuwa su zuba jari.

Sauran su ne Sashen Kula da Gandun Daji da kuma Dandalin Wasan Yara na Fadar Shugaban kasa.

Tijjani Umar ya sanar da haka ne a jawabinsa ga taron wata uku na farkon shekarar 2023 kan hadakar gwamnati da kamfanoni da ya gudana a Fadar Shugaban Kasa.

A watannin baya Shugaba Buhari ya sanya aikin gina sabbin bangarori na bayar da kulawa na musamman a asibitin a kasafin 2023.

A baya yanayin da Asibitin Fadar Shugaban Kasa ke ciki ya tayar da kura, musamman bayan da matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta yi korafi game da rashin magunguna da kayan aiki a asibitin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *