Iyayen daliban Najeriya da suka makale a Masar , suna neman ’ya’yan nasu su koma birnin Port Sudan na kasar ko za su samu jirgi zuwa Najeriya.

Iyayen daliban Najeriya da suka makale a iyakar kasar Masar bayan sun bar kasar Sudan mai fama da yaki, sun fara tunanin ’ya’yan nasu su koma birnin Port Sudan na kasar, ko za su samu jirgi zuwa Najeriya.

Duk da yakin da ake fama da shi a kasar ta Sudan, kawo yanzu dai ana ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama a birnin Port Sudan, duk da cewa an rufe sararin samaniya a wasu sassan kasar.

Iyayen daliban da suka kwana uku a kan iyakar kasar Masar ba tare da kasar ta ba su izinin shiga ba saboda rashin takardu, bayan sun baro Sudan saboda yaki, na ganin maimakon jiran gawon shanu, gara su nema wa ’ya’yan nasu mafita ta Port Sudan.

Suna tunanin cewa a Port Sudan, wanda yankin kasar Sudan ne za a samu jirgin da zai kwaso ’yan Najeriya zuwa gida, ga shi babu bukatar takardun neman izinin da suka hana su tsallakawa zuwa kasar Masar,
inda gwamnati ta tsara za su hau jirgi zuwa gida.

Gwamnatin Najeriya ta shirya kwashe ’yan kasar wadanda yaki ya ritsa da su a Sudan a motoci zuwa birnin Alkahira na kasar Masar, inda daga nan za a dauke su a jirgi zuwa gida.

Sai dai tun ranar Alhamis rukunin farko na ’yan Najeriyar da aka kwasodaga Khartoum, fadar kasar Sudan suka isa iyakar kasar Masar da ke Aswan, amma hukumomi sun hana su izinin tsallakawa saboda rashin
takardun da ya kamata.

Daliban da sauran ’yan Najeriyan da Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Khartoum ya kwaso, sun zargi jami’an ofishin da rashin yin abin da ya kamata domin sama musu izinin shiga kasar Masar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *