Buhari ya baiwa sojoji umarnin su tafi sudan domin aikin jigilar daliban Najeriya da suka makale acan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa sojoji umarnin su tafi sudan domin aikin jigilar daliban Najeriya da suka makale acan.

Shugaba Buhari ya bada umarnin ne a daidai lokacin yaki a kasar yakici yaki cinyewa sannan kuma daliban suke da korefe korafe akan gaza dawo dasu .

Rahotanni na cewa an tura jirgin sojin saman Najeriya yanzu haka domin yin wannan aikin mai muhimmanci na tabbatar da kwaso ‘yan Najeriya lafiya.

A cewar wani sakon Twitter da hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ta wallafa, jirgin sojojin zai tafi da abinci, da magani da kuma ruwa mai yawa domin tabbatar da inganta walwalar daliban a kan hanya ko acan kafin su dawo.

Sai dai rahotanni daga kan iyakar Sudan da Masar na nuni da cewa har yanzu mutrane sama da 7,000 ciki har da ‘yan Najeriya sun kasa shiga kasar ta Masar bayan da hukumomi suka hana su ketarawa.

Mutanen sun tserewa rikicin Sudan ne, inda suka nufi kasar ta Masar domin gwamnatocinsu su kwashe su daga kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *