Kwamishinan zabe na jihar Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa Ari, wanda lauya ne, ya bayyana cewa ya bayyana sakamakon zabe 69 a akwatinan zabe da aka sake a ranar 15 ga watan Afrilu saboda tursasawa.
Mun ta tattaro cewa Ari ya bayyana haka ne a cikin wata wasika da ya aikewa babban sufeton ‘yan sandan kasar inda ya bayyana irin rawar da ya taka a zaben gwamna mai cike da cece-kuce a ranar 16 ga watan Afrilu, wanda ya sanya ‘yar takarar jam’iyyar APC, Aishatu Ahmed (Binani) ta yi nasara a kan Dan takarar jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri.
A cikin wasikar wacce aka bada kwafi ga shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da kuma babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Ari ya bayyana cewa ya yi aiki ne a bisa ka’idar doka domin kaucewa hadarin da za a iya fuskanta na jinkiri wajen bayyana sakamakon zaben, musamman saboda ya lura cewa sakamakon da shugabanni suka kawo daga rumfunan zaben 69 da bai sanya wa hannu ba, ya sha bamban da wanda aka ɗora a shafin dora sakamakon zabe (IReV) na INEC.
Ari ya lissafo yunkurin maye gurbinsa a matsayin jami’in tattara bayanai tare da sakatariyar gudanarwa, barazanar da ‘yan takara suka yi na haifar da tarzoma, wasu kwamishinoni sun nada jami’an tattara sakamako da ba bisa ka’ida ba, da kuma kewaye gidansa da ‘yan sanda daga gidan gwamnati a matsayin wasu hadurra da ya fuskanta a lokacin gudanar zaben.
Ya ci gaba da cewa, “A kan haka ne na tattara dukkan sakamakon zaben na bayyana wanda ya lashe zaben bisa la’akari da mafi yawan kuri’un da yar takarar jam’iyyar APC ta samu.
“Na yi amfani da kuri’un da ‘yan takara biyun suka samu a zaben ta hanyar amfani da sakamakon zaben kamar yadda aka tattara a cikin dukkan nau’o’in EC8B, C, D da E da suka dace da nadawa bisa doka da kuma tantance jami’an tattara sakamakon zaben da kuma kaskantar da kai a matsayina na babban jami’in tattara zabe na jihar Adamawa kuma Kwamishinan Zabe (REC).
“Kafin sanarwar, akwai wani rahoton sirri da aka samu cewa kwamishinoni na kasa biyu suna gidan gwamnati, Yola da karfe 8:31 na dare ranar 15 ga Afrilun 2023 kuma sun gana da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.”
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Ya ce nan da nan bayan bayyana hakan ne wasu magoya bayan jam’iyyar PDP suka kai hari kan kwamishinonin INEC guda biyu da kuma jami’in bayyana zabe bisa zargin gazawar Gwamna Fintiri, inda ya kara da cewa “an yi zargin cewa mutanen da aka yi wa duka a cikin faifan bidiyo da aka ce sun so su kawo cikas a zaben jihar Adamawa ne da kuma canja ra’ayin jama’a kamar yadda aka bayyana ta hanyar zabe.”