TCN ya katse wasu layikan wutar KEDCO mai kula da jihohin Kano da Jigawa da Katsina kan rashin biyan bashi

TCN ya katse wasu layikan wutar KEDCO mai kula da jihohin Kano da Jigawa da Katsina bayan kokarinsa na ganin kamfanin ya biya bashin da ake bin ya faskara.

Mataimakin Janar-Manajan TCN na Shiyyar Kano, Bello Muhammad da kuma kakakin KEDCO, Sani Bala Sani, sun tabbatar cewa TCN ya katse wutar a ranar 26 ga watan Afrilu da muke ciki.

Layukan wutar da TCN ya kashe a Kano su ne Club Road da CBN da kuma Flour Mills (Dan Agundi), wanda hakan ya jefa yankunan da ke samun wuta daga nan a cikin duhu na tsawon kwanaki.

Tun ranar 24 ga watan ranar 24 ga wata Babban Jami’in Kasuwanci na TCN, E. A. Eje ya sanar cewa, “TCN ya ba da umarnin katse wutar KEDCO saboda saba ka’idar biyan bashi.

Ya bayyana cewa katse layikan somin-tabi ne kafin TCN ya katse wutar gaba daya idan kamfanin bai biya bashin ba.
Amma mai magana da yawun KEDCO, Sani Bala Sani, ya ce, “Duk da
haka, kamfanin na aiki tare da TCN da sauran masu ruwa da tsaki
domin ganin an daidaita nan ba da jimawa ba.”
Sani ya ba wa jama’a hakuri, da alkawarin tabbatar da sama musu
wutar lantarki mai inganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *