Rukunin farko na ’yan Najeriya da yaki ya ritsa dasu a Sudan za su isa Abuja yau

Gwamnatin Tarayya ta ce rukunin farko na ’yan Najeriya da yaki ya ritsa da su a kasar Sudan za su isa Abuja a wannan rana ta Juma’a

Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Ketare, Abike Dabiri- Erewa ta ce mutum 1,500 ne ake saran isowar su, a Abuja a ranar ta Juma’a.

Shima da yake jawabi,kakakin Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Ezekiel Manzo, ya tabbatar da cewa a wannan rana rukunin farko na ’yan Najeriyar da suka makale a Sudan za su fara sauka a Abuja.

Abike ta bayyana cewa za a bayar da fifiko ga mata da kananan yara da dalibai daga cikin ’yan Najeria miliyan uku da ke Sudan kuma gwamnati na yin iya kokarinta domin kwaso su zuwa gida.

Erewa wacce ta bayyana hakan a tashar talabijin ta Channels tace wasu jami’o’in Najeriya sun yi tayin daukar daliban da suka dawo daga Sudan domin ci gaba da karatunsu a gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *